Home Labaru Siyasar Majalisa: Kakakin Apc Ya Ce Al’ummar Ibo Su Suka Yi Wa...

Siyasar Majalisa: Kakakin Apc Ya Ce Al’ummar Ibo Su Suka Yi Wa Kan Su Sagegeduwa

300
0

Kakakin jam’iyyar APC na kasa Yekini Nabena ya ce babu wani laifi idan al’ummar Ibo sun rasa manyan mukamai a zauran majalisun tarayya.

Nabena ya ce laifin al’ummar yankin Kudu maso Gabas shine kin marawa jam’iyyar APC baya a zaben 2019, wanda hakan ya yi sanadiyar maida ‘yan majalisar da su ka fito daga yakin saniyar warewa wajen rabon mukamai masu tsoka a zauran majalisar.

Wadannan kalamai dai, na zuwa ne a matsayin martani a kan kukan da Sanata Orji Uzor-Kalu ya yi cewa, zai yi takarar shugaban majalisar dattawa idan har APC ta hana shi kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa da ya ke hari.

Nabena ya ce mutanan Kudu ta Gabas sun marawa Atiku Abubakar baya ne a zaben da ya gabata, don haka babu laifi don APC ta kebe ‘yan majalisar da su ka fito daga wannan shiyya wajen zakulo wadanda za su rike shugaban majalisardattawa.

A karshe Nabena ya yiwa sanata Kalu hannunka mai sanda a kan cewa, babu wanda zai hana shi takarar neman kujerar shugaban majalisar dattawa, amma ya sani cewa ba zai kai labari ba.

Leave a Reply