Home Labaru Siyasar Kogi: Dino Melaye Ba Zai Iya Yin Galaba A Kai Na...

Siyasar Kogi: Dino Melaye Ba Zai Iya Yin Galaba A Kai Na Ba – Yahaya Bello

662
0

Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi, ya tofa albarkacin bakin sa a kan kudirin Sanata Dino Melaye na zama gwamnan jihar Kogi a zabe da za a yi ranar 16 ga watan Nuwamba na shekara ta 2019.

Yahaya Bello ya ce, tabbas abin da Dino Melaye ke shirin yi ba abu ne mai sauki gare shi ba.

Gwamna Yahaya Bello ya bayyana haka ne yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai.Ya ce kamata ya yi Dino Melaye ya fara cika alkawarin da ya yi wa yankin sa kafin ya ya ce zai yi takara da shi, domin yin hakan tamkar Daukar-Dala ne ba gammo.

Leave a Reply