Home Labaru Siyasar Kano: Wata Kungiya Ta Bukaci Ganduje Ya Sauke Masu Yada Labaran...

Siyasar Kano: Wata Kungiya Ta Bukaci Ganduje Ya Sauke Masu Yada Labaran Sa

274
0

Wata kungiya mai zaman kanta a Kano, Renaissance Coalition ta shawarci gwamnatin Jihar ta kori sakataren yada labaran Gwamna Abdullahi Ganduje saboda yadda ya tafiyar da batun rikicin da ke tsakanin gwamnan da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.
Kakakin kungiyar, Ibrahim A. Waiya ya yi wannan kirar ne yayin da ya ke mayar da martani kan wani jawabi da aka ce sakataren yada labarai na gwamnan Abba Anwar ya yi kan sulhun da Aliko Dangote da kungiyar gwamnonin Najeriya ke yi tsakanin shugabanin biyu.
Ana zargin sakataren yada labarai na gwamnatin da cewa ba a fara sulhu ba tsakanin sarki da gwamna wanda kungiyar na ganin hakan na da hatsari kuma barazana ce ga zaman lafiya a jihar.
A cewar Waiya, “A matsayin mu na ‘yan asalin Kano masu son zaman lafiya, muna mamakin yadda wasu ke kokarin ganin rikicin da ke tsakanin sarki da gwamnan Kano ta cigaba duk da cewa hakan na iya kawo tabarbarewar tsaro a Najeriya.
“Babban matsalar mu shine wasu da aka daura wa alhakin yin magana a madadin gwamnatin Kano da suka hada da Salihu Tanko Yakasai da Aminu Isah Abba Anwar cikin ‘yan kwana kin nan suka nuna rashin kwarewa a cikin aikinsu yayin da suka yi ikirarin cewa ba a yi sulhu ba tsakanin gwamna da sarkin Kano.