Home Labaru Siyasar Kano: Abba Gida-Gida Na Zargin INEC Da Shirya Masu Gadar-Zare

Siyasar Kano: Abba Gida-Gida Na Zargin INEC Da Shirya Masu Gadar-Zare

1493
0

Dan takarar kujerar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar PDP Abba Kabir Yusuf, ya nuna rashin jin dadi a kan tsaiko daga bangaren hukumar zabe na hana jam’iyar sa ta binciki kayayyakin da aka yi aiki da su wajen zabe.

Abba Yusuf, wanda aka fi sani da Gida-Gida, ya ce hukumar zabe ta kirkiri tsaikon ne da gangan, saboda ta na so ta hana jam’iyyar PDP hakkin ta na binciken kayayyakin zaben.

Gida-Gida ya bayyana haka ne, yayin da ya ke tattaunawa da manema labarai a ofishin zabe da ke Kano, inda ya je domin samo dalilin tsaikon da ake samu, sai dai bai samu jami’in hukumar ko daya da zai iya sauraron korafin da ya je da shi.

Ya ce idan ba a manta ba, tun daga lokacin da su ka shiga kotu, sun nemi a ba su damar binciken kayayyakin zaben da hukumar zaben ta yi amfani da su a zaben gwamna, amma duk da kotun ta ta bada izini har yanzu abin ya na tafiyar hawainiya.

A karshe ya ce, hukumar zaben korar su su ka yi daga harabar ofishin su, tare da cewa su koma kotu a sake ba su wani izinin domin wa’adin da aka ba su a yanzu ya riga ya kare.

Leave a Reply