Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Siyasar Kaduna: Mutanen Mr La 9 Sun Bada Shaida A Gaban Kotu

Lawal Adamu Mr La, Dan Takarar Kujerar Sanata Na Jam’iyyar PDP

A zaman kotun sauraren shari’ar zaben kujerar dan majalisar dattawa na mazabar Kaduna ta tsakiya, wakilan jam’iyyar PDP 9 ne su ka bada shaida a gaban kotun.

Dan takarar kujerar sanata na jam’iyyar PDP Lawal Adamu Mr La, ya garzaya kotu domin kalubalantar nasarar da Uba Sani na Jam’iyyar APC ya yi a Zaben da ya gabata.

Jam’iyyar PDP dai ta ce an yi aringizon kuri’u a mazabu da dama a zaben sanatan Kaduna ta tsakiya.

Wadanda su ka bada shaidar sun ce, a mazabun da su ka yi aiki da su ka hada da mazabar Magajin Gari da karamar hukumar Birnin Gwari, sun ce aringizon da aka yi ba ya misaltuwa, domin har da jami’an tsaro ake hada baki wajen dankare akwatunan zabe da kuri’un karya.

Baya ga mutanen tara da su ka bada shaidar, Mr La, ya ce akwai wasu mutane 96 da za su bayyana a gaban kotun domin bada shaida da kuma fadin yadda aka rika aringizon kuri’u a mazabun kananan hukumomi shida na mazabar Kaduna ta tsakiya.

Exit mobile version