Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta ksa INEC, ta mallakawa tsohon gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha takadar shaidar cin zaben kujerar Sanata da aka gudanar a watan Fabrairu.
Idan dai ba a manta ba, hukumar INEC a baya ta hau kujerar naki wajen mallakawa Rochas Okorocha takardar shaidar cin zabe, sakamakon zargin sa da tursasawa kwamishinan zaben jihar Farfesa Innocent Ibeabuchi sanar da nasarar da ya samu.
Babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Juma’ar da ta gabata ne, ta umurci hukumar zabe ta kasa da ta gaggauta mallaka wa tsohon gwamna Okorocha takardar shaidar lashe zaben kujerar sanata ta shiyyar Imo ta Yamma.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, Okorocha ya mika godiyar sa cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa, Sam Onmuemedo ya gabatar yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a birnin Owerri.