Home Labaru Siyasar Bayelsa: Mai Kyakkyawar Manufa Kawi Zai Gaji Kujera Ta – Dickson

Siyasar Bayelsa: Mai Kyakkyawar Manufa Kawi Zai Gaji Kujera Ta – Dickson

482
0

Gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson, ya ce al’ummar jihar sa ba za su taba zaben wanda babu burburshin imani a zuciyar sa a matsayin zai gaji kujerar sa ta gwamna ba.

A cikin jawabin da ya gabatar yayin kammala taron addu’o’i da azumin kwanaki uku da aka gudanar a birnin Yenagoa na jihar Bayelsa, Dickson ya ce dole magajin kujerar sa ya kasance mai tsarkakakkiyar zuciya.

Ya ce jihar Bayelsa ba za ta sake kasancewa a karkashin jagorancin miyagun dabi’u na kauce wa hanya irin su tsubbace-tsubbace da zubar jinin al’umma da kuma tada zaune tsaye.

Gwamnan, ya kuma bukaci al’ummar jihar su kaurace wa shiga sabgogin kungiyoyin asiri, sun a yaudarar su zuwa halaka domin cimma wasu bukatu na kashin kan su.

Dickson ya kara da cewa, magajin kujerar sa zai kasance zakakurin gaske, kuma mai akidar tabbatar da ci-gaban tsare-tsare da manufofin dimokradiyya na jam’iyyar PDP.

Gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson

Leave a Reply