Home Labaru Siyasar Adamawa: Fintiri Ya Sha Alwashin Binciken Gwamnatin Bindow

Siyasar Adamawa: Fintiri Ya Sha Alwashin Binciken Gwamnatin Bindow

424
0

Zababben Gwamnan Jihar Adamawa Ahmadu Fintiri, ya ce a shirye ya ke ya binciki duk wanda ake zargin ya yi rashin gaskiya a karkashin mulkin Jibrilla Bindow mai barin gado.

Fintiri ya bayyana haka ne a Yola, a lokacin da ya ke karbar rahoto mai dauke da shafuka 67 da Kwamitin Karbar Mulki ya mika ma shi.

Ya ce binciken da kwamitin ya gudanar ya nuna akwai wurare da dama da aka yi almubazzaranci da kudaden gwamnati, don haka ya ce ba zai yiwu sabuwar gwamnatin da zai kafa ta kauda kai daga wannan tabargaza da aka tafka ba.

Fintiri ya cigaba da cewa, ba za su kauda kai daga wuraren da aka karya doka ko wuraren da aka yi facaka da kudaden mutane ba.

Ya nuna takaicin yadda gwamnati mai barin gado ta karbi kusan naira biliyan 332 a cikin shekaru hudu daga gwamnatin tarayya, amma babu wani abin kirkin da za a iya gani a nuna a cikin jihar da za a iya tutiya da shi ba.

Da ya ke mika rahoton, Shugaban Kwamitin Aliyu Ismaila, ya ce gwamnatin Bindow ta yi raga-raga da jihar Adamawa, kuma ta bar dimbin bashi har na naira biliyan 115

Leave a Reply