Home Labaru Siyasar 2023: Ni Zan Gaji Shugaba Muhammadu Buhari – Bakare

Siyasar 2023: Ni Zan Gaji Shugaba Muhammadu Buhari – Bakare

534
0
Fasto Tunde Bakare, Babban Limamin Cocin Da Ke Legas
Fasto Tunde Bakare, Babban Limamin Cocin Da Ke Legas

Babban Limamin cocin ‘ Latter Rain Assembly’ da ke Legas Fasto Tunde Bakare, ya bada tabbacin cewa shi zai gaji shugaba Muhammadu Buhari a shekara ta 2023.

Kamar yadda rahotanni su ka bayyana, Faston ya ce da zarar shugaba Buhari ya kammala wa’adin mulkin sa shi zai gaje shi.

Babban Faston ya cigaba da cewa, wadanda ba su da labari su sani cewa, shugaba Buhari ne shugaban kasa na 15 a Nijeriya, yayin da shi kuma zai kasance na 16.

Buhari ya sa hannusa ya dafa a kirji yana cewa: “Ina so ku san wannan a safiyar nan cewa babu abin da zai iya canza wannan kadara da sunan Ubangiji.

Idan dai ba a manta da tarihi ba, shugaba Buhari ya taba tsayawa takara tare da Tunde Bakare a matsayin mataimakin sa a zaben shekara ta 2011 karkashin tsohuwar jam’iyyar CPC.

Leave a Reply