Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Siyasa: Majalisar Dokokin Jihar Zamfara Ta Umarci Mataimakin Gwamnati Ya Bayyana A Gaban Ta

Majalisar dokokin jihar Zamfara ta bai wa mataimakin gwamnan jihar wa’adin awanni 48 ya bayyana a gabanta kan zargin aikata ba daidai ba.

Majalisar na tuhumar Barista Mahadi Aliyu Gusau kan wani gangami siyasa a ranar 10 ga watan Juli, duk da yake ‘yan bindiga sun kai hari a karamar hukumar Maradun a daidai wannan lokacin.

Wannan na zuwa ne wata guda bayan mataimakin gwamnan ya ki bin Gwamna Bello Matawalle wanda ya sauya sheka daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa Jam’iyyar APC mai mulki a watan na Yuni.

Tun daga wancan lokacin ake takun-saka tsakanin gwamnan na jihar Zamfara da mataimakinsa, inda ya gargade shi kan ba zai dauki duk wani raini daga gare shi ba.

Har wa yau, wasu na ganin kiran da majalisar ta yi wa Mahadi Gusau na da alaka da taron da jam’iyyar PDP ta gudanar a jihar Bauchi a karshen mako, wanda Mahadi ya halarta tare da jaddada wa jam’iyyar cewa yana nan daram a cikinta.

Exit mobile version