Gwamnonin Jam’iyyar APC mai mulki sun buƙaci gwamna Mai Mala Buni da ke jagorancin kwamitin riƙon kwaryar da ke tafiyar da harkokin jam’iyyar ya gaggauta gudanar da taronsu na kasa da zai bada damar zaɓen jagorori a kananan hukumomi da jihohi.
Wannan bukata ta su na kunshe a cikin wata sanarwa da suka fitar dauke da sa hannun gwamnan Kebbi kuma shugaban kungiyar gwamnonin APC, Atiku Bagudu.
Kwamitin ya gudanar da zabukan mazabu, wanda ke cike da ce-ce-ku-ce kan zargin rashin sahihanci da kura-kurai a kwanakin baya.
Gwamnonin sun kuma bukaci likitoci masu neman kwarewa su janye daga yajin aikin da su ka shiga a faɗin ƙasar.
Sun kuma yi kira ga mahukunta su yi kokarin daidaitawa da likitoci ganin yadda yajin aiki ke tasiri ga fanin lafiya a ƙasar.
You must log in to post a comment.