Shugaban jam’iyyar APC ta kasa, Adams Oshiomhole, ya ce bayan mukamin shugaban majalisar dattawa da na kakakin majalisar wakilai da aka riga a kasabta, ba a riga an yi rabe-raben sauran mukamai ba.
Oshiomhole, ya bayyana cewa ana duba yiwuwar ba yankin kudu maso kudu mukamin mataimakin shugaban majalisar dattawa.
Oshiomhole wanda ya sami wakilcin mai magana da yawunsa Simon Egbebulem, ya ce ba a riga an raba manyan mukaman majalisar ba,. Sai dai rahotannin sun nuna cewa tu ni an mika mukamin ga na hannun damar Oshiomhole, Sanata Francis Alimehkena, wanda aka sake zaba domin wakiltan Edo ta Arewa a majalisar dattawa.