Home Labaru Shugabannin APC Na Shirin Tsaida Gwamna Lalong Takarar Shugaban Ƙasa

Shugabannin APC Na Shirin Tsaida Gwamna Lalong Takarar Shugaban Ƙasa

185
0

Shugabannin jam’iyyar APC na jihar Filato, sun yanke hukuncin mara wa gwamna Lalong baya ya nemi kujerar shugaban kasa a zaben shekara ta 2023.

Yayin ganawar su a birnin Jos, shugabannin sun kuma tattauna a kan rikicin da ke wakana a majalisar dokoki ta jihar Filato.

Shugabannin dai sun ce, Gwamna Lalong ya san hanyoyin shawo kan matsalolin siyasa, shi ya sa ma rikicin majalisar dokoki ta jihar bai yi muni ba.

Daya daga cikin shugabannin jam’iyyar Saleh Mandung Zazzaga, ya ce gwamna Lalong zai ɗaga martabar Nijeriya zuwa inda mutane ba su yi tsammani ba.

Ya ce sun yi hasashen ne, duba da nasarorin da gwamnan ya samu na rikice-rikice da yadda ya shawo kan sabanin da ake samu na ƙabilanci da addini a fadin jihar Filato.

Leave a Reply