Wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar PDP sun fara tuntubar sabbin ‘yan majalisar wakilai da na dattawa domin ganin an gudanar da zaben sabbin shugabannin majalisun cikin lumana.
Wata majiya ta ce shugabannin na PDP su na son ganin ‘yan jam’iyyar su a majalisu biyu na tarayya sun jingine duk wata niyya ta nuna hamayya a kan ‘yan takarar shugabancin majalisa da jam’iyyar APC ke so a zaba.
Daga cikin wadanda su ka bijiro da wannan mataki sun hada da wasu daga cikin sabbin zababbun gwamnoni, da gwamnoni masu barin gado da wasu shugabannin jam’iyyar PDP.
Bayan shugabanni da jagororin jam’iyyar PDP, rahotannin sun ce akwai wasu manyan ‘yan Nijeriya da ba ‘yan siyasa ba da ke kokarin ganin an gudanar da zaben shugabannin majalisar cikin salama.
Wani daga cikin manyan ‘yan jam’iyyar PDP, ya ce zai iya tabbatar da cewa shugabannin majalisa na yanzu da shugabannin jam’iyyar PDP sun sha zama tare da wasu manya Nijeriya domin tattauna yadda za a gudanar da zaben shugabannin majalisa na gaba cikin lumana.