Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Shugabancin Majalisar Dattawa: Dalilin Da Ya Sa Muka Ce Sai Yari- Injiniya Kailani

Gamayyar kungiyoyin jamiyyun APC da aka fi Sani da Conferedation of all support Group, ta tsaya Kai da fata cewar tsohon gwamnan jihar Zamfara sanata Abdulazee Yari, shine ya fi kowa cancanta ya shugabanci zauren majalisar dattawa a majalisa ta 10.

A cewar Kungiyar daga cikin wadanda ke Neman shugabancin majalisar dattawan, Abubakar  Yari, ne ya fi dacewa saboda kwarewar sa a bangaren harkokin siyasar Najeriya.

Shugaban kungiyar Injiniya Kailani, ya ce ‘ya’yan Jamiyyar APC na da damar bayyana ra’ayin su kamar yadda kundin tsarin mulkin dimkoradiyya ya tanadar masu.

Ya ce tuna lokacin da Jamiyar su ta APC a karkashin jagorancin Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ta sami kuria milliyan 8, yankin arewa maso yamma ta samar da kashi 30  cikin kuri’un da Tinubu ya samu a Najeriya, yankin da shugaban kasa Tinubu ya fito wato yankin kudu maso yamma ta samar da kur’a kashi 25 ne.

Injiniya Kailani, ya ce yankin arewa ta tsakiya ce ta samar da Kashi 20, sai Kuma  arewa maso gabas Kashi 13, sannan yankin kudu maso kudu ya samar da Kashi 9 sai kudu maso gabas ya samar da Kashi 1, Wanda ya nuna cewar yankin da Yari ya fito ne ya bada Kuria Mafi tsoka.

Shugaban kungiyar Injiniya Kailani Muhammad, ya bukaci mataimakin shugaban kasa Kashim Shattima, da sauran ‘Yan kwamitin gudanrwa su kaucewa daukidora a shugabancin Majalisar domin ayi abinda ya dace, ya ce mulkin dimkoradiyya mulki ne da adadin mutanen ka ke baka.

Exit mobile version