Home Labaru Shugabancin Majalisa: Mutanen Borno Na Tare Da Sanata Ndume – Jigon APC

Shugabancin Majalisa: Mutanen Borno Na Tare Da Sanata Ndume – Jigon APC

492
0
Sanata Ali Ndume
Sanata Ali Ndume

Jagoran kungiyar yakin neman zaben shugaba Muhammadu Buhari da Osinbajo Usman Ibrahim, ya bukaci Sanata Ali Ndume cewa kada ya janye daga takarar kujerar shugabancin majalisar dattawa.

Kamar yadda ya shaida wa jaridar Leadership a Abuja, Ibrahim ya ce al’ummar jihar Borno su na da bukatar Ndume ya zama shugaban majalisar dattawa.

Ya ce kungiyar su za ta yi taro a Abuja domin bayyana wa al’umma goyon bayan ta ga kudirin Ndume, inda ya ce dan majalisar ya na bukatar ramuwar biyayyar da ya yi wa gwamnatin shugaba Buhari.A wani bangaren kuma, rahotanni sun ambato Sanata Suleiman Hunkuyi ya na cewa, tsaida dan takara guda daya a matsayin shugaban majalisa ba tsarin damokardiyya ba ne.

Leave a Reply