Rahotanni na cewa, ‘yan majalisar wakilai da dama sun daura damarar neman kujerar shugaban majalisar Yakubu Dogara.
Daga cikin masu neman kujerar kuwa akwai dan majalisa Ahmed Idris Wase, da Umar Mohammed Bago, da Abdulrazak Namdas, da Babangida Ibrahim da Muktar Aliyu Betara da John Dyegh daga jihar Benue.
A tarihin siyasar Nijeriya tun a shekara ta 1999 dai, Yankin Arewa ta tsakiya bai taba samun mukamin kujerar shugaban majalisar wakilai ko mataimakin sa ba.
Jam’iyyar APC dai ta bayyana cewa, dan majalisa Femi Gbajabiamila daga jihar Legas ta ke so ya gaji Yakubu Dogara a matsayin shugaban majalisar ta 9.