Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Shugabancin Majalisa: Ahmad Lawan Ya Gana Da Sanatocin PDP

Sanata Ahmad Lawan

Sanata Ahmad Lawan

Dan takarar kujerar shugabancin majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan ya gana da wasu gwamnonin jam’iyyar PDP a wani mataki na ganin ya samu hadin kai wajen lashe zaben shugabancin majalisar.

Matakin da ya sabawa matsayar shugabanin jam’iyyar APC, wanda a baya suka ce ba bu bukatar suka kai da jam’iyyar PDP domin zaben shugaban majalisar.

Zaben sanata Ahmad Lawan da Kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC ta yi ya janyo rabuwar kai, wanda daga bisani  sanata Ali Ndume da Danjuma Goje suka bijire cewa, suma za su yi takarar. Idan dai ba a manta ba, bayan kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC ta zabi Lawan a matsayin dan takarar sa, shugaban jam’iyyar na kasa Adams Oshiomhole ya ce ba su bukatar ‘yan majalisun jam’iyyar PDP domin samun nasarar lashe zaben kujeru a majalisar dattawa.

Exit mobile version