Home Home Shugabancin Jam’iyyar APC: Wakilai Daga Sassa Daban-Daban Sun Amince Da Zabin Shugaban...

Shugabancin Jam’iyyar APC: Wakilai Daga Sassa Daban-Daban Sun Amince Da Zabin Shugaban Kasa

106
0
Wakilan jam’iyyar APC daga sassa daban-daban na Najeriya sun amince da tsohon gwamnan jihar Nasarawa Sanata Abdullahi Adamu a matsayin sabon shugaban jam'iyyar mai mulki a Najeriya.


Wakilan jam’iyyar APC daga sassa daban-daban na Najeriya sun amince da tsohon gwamnan jihar Nasarawa Sanata Abdullahi Adamu a matsayin sabon shugaban jam’iyyar mai mulki a Najeriya.

Gwamnan jihar Jigawa Muhammadu Badaru, ne ya sanar da hakan a yayin babban taron jam’iyyar bayan duk waɗanda suke takara sun janye wa Abdullahi Adamu.

Sanata Abdullahi Adamu, wanda da farko ba ya cikin waɗanda suka nuna sha’awar takarar shugabancin APC, daga bisani ne ya kutso kai kuma ya samu goyon bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, da wasu gwamnoni.

Goyon bayan da Sanata Abdullahi Adamu ya samu ya tilasta wa sauran ƴan takarar shugabancin APC janye wa a ranar Asabar kafin shiga dandalin taron.

Ƴan takarar da suka janye dai sun hada da tsohon gwamnan jihar Benue George Akume, da tsohon gwamnan jihar Nasarawa Tanko Al-Makura, da tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul’Aziz Yari Abubakar, da Saliu Mustapha da kuma Etsu Muhammed.