Home Home Shugabancin APC: Ganduje Ya Samu Goyon Baya Daga Tsaffin Gwamnoni

Shugabancin APC: Ganduje Ya Samu Goyon Baya Daga Tsaffin Gwamnoni

91
0

A wani yunkuri na nuna shirin sa da bajintar sa na zama shugaban jam’iyyar APC na kasa, tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ziyarci wasu tsoffin gwamnonin jam’iyyar ta APC.

Tsoffin gwamnonin da ya ziyarta sun hada da Muhammad Bello Matawalle tsohon gwamnan jihar Zamfara, da Mallam Nasir Elrufa’i tsohon gwamnan jihar Kaduna, da Simon Lalong tsohon gwamnan jihar Filato, da kuma Abubakar sani Bello tsohon gwamnan jihar Neja.

A wani zama da shugabannin jam’iyyar APC na jihohin Arewa maso yamma da suka hada da Kaduna, da Katsina, da Sokoto, da Zamfara, da Kebbi da kuma Jigawa suka yi a jihar Kaduna, sun rattaba hannu kan goyon bayan su ga Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa.

Shugabannin jam’iyyar, sun ce, sun yanke shawarar goyon bayan Ganduje ne bisa la’akari da rawar da ya taka wajen wayar da kan al’ummar Arewa sanin muhimmancin dan takarar da jam’iyyar ta tsayar a zaben da ya gabata, wanda hakan ya kai ta ga cin  Nasara.

Leave a Reply