Home Labaru Shugabanci Majalisa: Buhari Ya Taya Sabbin Shugabanni Murnar Lashe Zabe

Shugabanci Majalisa: Buhari Ya Taya Sabbin Shugabanni Murnar Lashe Zabe

272
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya daukacin sabbin zababbabun shugabannin majalisar dokokin tarayya ta tara murnar nasarar lashe zaben da su ka yi a ranar Talatar da ta gabata.

Buhari ya bayyana nasarar a matsayin wata sabuwar ci-gaba da Nijeriya za ta samu sabanin nakasu da bangaranci da majalisa ta 8 ta fuskan ta.

Shugaban kasa Buhari ya kuma yabawa daukacin ‘yan majalisa da jam’iyyun su akan nuna soyayyar su ga Nijeriya kafin zabe da bayan zabe, sannan ya nuna farin cikin sa a kan irin salon da aka yi amfani da shi wajen gudanar da zaben, inda ya ce wannan babban nasarace ga demokradiyyar Nijeriya.

Buhari ya kuma yi kira ga wadanda suka yi nasara a zaben su yi amfani kujerar su wajen fifita manufar Nijeriya da al’ummar da kuma cigaban demokradiyya kafin na su, sannan ya bukaci wadanda suka fadi zaben su hada karfi da karfe da shugabannin su wajen kawo cigaba a kasa.

Leave a Reply