Home Labaru Shugabanci: Dole A Fidda Nijeriya Daga Kangin Talauci – Ahmed Lawan

Shugabanci: Dole A Fidda Nijeriya Daga Kangin Talauci – Ahmed Lawan

505
0
Sanata Ahmed Lawan, Shugaban Majalisar Dattawa
Sanata Ahmed Lawan, Shugaban Majalisar Dattawa

Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan, ya ce ya zama dole majalisar zartarwa da majalisar dokoki ta tarayya su hada kai domin fidda ‘yan Nijeriya daga kangin talauci.

Sanata Ahmed Lawan, ya ce akwai tsabar talauci a kasar nan, kuma sai majalissun tarayya sun hada gwiwa sannan a iya magance lamarin.

Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan

Idan dai za a iya tunawa, a baya Sanatan ya ba ‘yan Nijeriya tabbacin kawo sauyi a kamfanin man fetur da gas na Nijeriya.

Ya ce ya na ta ganawa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari akan kalubalen da Nijeriya ke fuskanta, kuma zai cigaba da fafutukar ganin an samu mafita a matsayin sa na shugaban majalisar dattawa.

Leave a Reply