Home Labaru Shugabanci: Buhari Ya Tabbatar Da Adamu A Matsayin Shugaban ‘Yan Sandan Nijeriya

Shugabanci: Buhari Ya Tabbatar Da Adamu A Matsayin Shugaban ‘Yan Sandan Nijeriya

415
0
Mohammed Adamu, Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya
Mohammed Adamu, Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da Muhammad Adamu a matsayin shugaban hukumar ‘yan sandan Nijeriya mai cikakken iko.

Buhari ya tabbatar da Muhammad Adamu ne a matsayin shugaban hukumar ‘yan sandan Nijeriya a wani taro da ya gudana a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Shugaban ma’aikatan hukumar ‘yan sanda Musuliu Smith da gwamnonin Nijeriya 36 su na daya daga cikin wadanda suka halarci taron tabbatar wan.

Idan dai ba a manta ba, Muhammad Adamu ya karbi ragamar huukumar ‘yan sandan Nijeriya ne a ranar 15 ga watan Junairun shekara ta 2019 daga hannun wanda gabace shi Ibrahim Idris.

Gwamnan jihar Ekiti Koyode Fayemi da ya ke jawabi a wajen taron, ya ce Muhammad Adamu ya samu sahalewar zama cikakken shugaban ‘yan sandan Nijeriya ne bayan wata tattaunawa da hukumar ‘yan sanda ta yi a kan kwarewar sa da kuma jajircewar sa a aikin dan sanda.

A nashi bangaran Muhammad Adamu ya yi al’kawarin samar da wata runduna ta musamman da za ta yi aiki tukuru domin magance duk wani kalubale da ya jibanci matsalar tsaro a Nijeriya.