Jalal Arabi ya mika ta’aziyya ga ‘yanuwa da iyalan Marigayya Hajiya Tawakaltu daga Jihar Kebbi, da ta rasu a Makkah.
Wakilin Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Nijeriya a garin Makkah Dr Aliyu Tanko ya mika sakon a madaddin Shugaban.
A jawabin sa wajen ta’aziyyar, ya bayyana cewa, mutuwa na kan kowa a koyaushe kuma a ko ina.
Alhaji Garba , ya nuna jin dadin kan yadda Shugaban ya aiko wakilin sa da jami’an sa domin taya su alhinin wannan rashin.
wannan abin a yaba ne. Zuwa yanzu hukumar NAHCON ta kwashe maniyyata 20,974 daga Najeriya zuwa saudiyya