Home Home Shugaban Kasa: Jam’Iyyar PRP Ta Kaddamar Da Kwamitin Yakin  Neman Zabe

Shugaban Kasa: Jam’Iyyar PRP Ta Kaddamar Da Kwamitin Yakin  Neman Zabe

28
0

Jam’iyyar PRP, ta kaddamar da kwamitin yakin zaben shugaban kasa a zaben 2023.

A ranar Asabar 12 ga watan Nuwamba ne jam’iyyar PRP,ta kaddamar da kwamitin nata nay akin neman zaben dan takaranta na shugaban kasa.

A yayin kaddamar da kwamitin, jam’iyyar ta PRP ta bayyana kudurorin ta ga al’ummar Najeriya da zata yi amfani da su wajen kawo sauyi ga rayuwar ‘yan kasa idan ta samu nasara a zaben.

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar ta PRP, Kola Abiola, ya bayyana manufofin jam’iyyar a wajen taron, in da ya fara da batun bunkasa tattalin arzikin kasa.

Mr Kola Abiola, ya ce, bunkasa noma da kiwo, da ilimi, da tsaro dama bunkasa ma’adinun kasa na daga cikin manufofin jam’iyyar su ta PRP.