Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa Farfesa Rufa’i Alƙali ya ajiye muƙamin sa.
A cikin wata wasiƙa da ya aike wa sakataren jam’iyyar na ƙasa, Farfesa Alƙali ya ce ya ajiye muƙamin sa ne domin a ba sabbin jini dama, ta yadda za su ɗora a kan ci-gaban da jam’iyyar ta samu cikin kankanin lokacin da ya yi ya na jagorantar ta.
Alƙali ya ce, la’akari da irin abubuwan da su ka faru kafin zaɓubbukan da su ka gabata da kuma okacin zaɓe, ya na cike da fatan cewa jam’iyyar ta na da makoma mai kyau.
Ya ce ya na cike da fatan jam’iyyar za ta kasance cikin manyan jam’iyyun da za su iya cin zaɓen shugaban ƙasa da sauran muƙamai a zaɓen shekara ta 2027.
Farfesa Rufa’i Alƙali, ya ce jam’iyyar ta na buƙatar sauye-sauye da dama ta fuskar shugabanci a matakai daban-daban domin ƙara ƙarfafa matsayin ta.
You must log in to post a comment.