Home Labaru Shugaba Tinubu Zai Yi Balaguronsa Na Farko

Shugaba Tinubu Zai Yi Balaguronsa Na Farko

85
0

Shugaban kasa Bola Tinubu, zai yi balaguron sa na farko
zuwa kasar Faransa a ranar Alhamis mai zuwa, domin halartar
taron nazari tare da sa hannu a kan yarjejeniyar samar da
kudade ga kananan kasashen duniya.

Mataimaki na musamman ga shugaban kasa a kan harkokin yada labarai da tsare-tsare Dele Alake ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Tinubu zai ziyarci kasar Faransa ne bisa rakiyar wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin sa domin halartar taron, wanda zai gudana a karkashin jagorancin shugaba Emmanueel Macron.

Shugaba Tinubu zai halarci taron na tsawon kwanaki biyu, wanda zai maida hankali a kan cike gurbin rashin kudi ga kasashe musamman matalauta da ke fuskantar kalubale daban-daban, wadanda su ka hada da bashi da sauyin yanayi da karancin masu zuba jari baya ga bunkasar tattalin arziki.

Tinubu da sauran takwarorin sa na kasashen duniya da manyan kamfanonin kasa da kasa da masana harkokin kudade da masana tattalin arziki za su yi nazari mai zurfi a kan yadda za a farfado da tattalin arzikin kananan kasashen da suka yi fama da tasirin annobar Covid-19 da tsananin talauci

Leave a Reply