Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya gayyaci gwamnonin Nijeriya 36 domin yin wani muhimmin taro a fadarsa da ke Abuja.
Rahotanni sun ce taron zai gudana ne kafin Shugaban kasa Tinubu ya wuce birnin Addis Ababa na kasar Habasha, domin halartar taron ƙungiyar Tarayyar Afirka AU.
Taron dai zai kasance irinsa na biyu tun bayan da shugaba Tinubu ya hau karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayu, sannan za a tattauna ne kan matsalar ƙalubalen tattalin arziƙi da rashin tsaron da ya addabi Nijeriya.
Bayanin haka na kunshe a wani sako da jaridar Arise TV ta wallafa a shafinta na Twitter, tare da cewa taron na zuwa ne bayan gwamnonin PDP sun soki manufofin Tinubu kan tattalin arziƙi da kuma yadda rayuwa ta yi tsada a Nijeriya.
Idan ba a manta ba, gwamnonin PDP sun yi tsokaci a kan hauhawar farashin kayayyaki da ƙaruwar yunwa da aikata laifuka da kuma yawan mace-macen da ake fama da su a Nijeriya.
Sai dai fadar shugaban ƙasa ta maida martani a kan tsokacin na PDP, inda ta soki gwamnonin a kan yadda suke gudanar da ayyukansu, musamman ganin yadda suka kasa biyan albashi duk da ƙarin kason da gwamnatin tarayya ke ba su.