Home Home Shugaba Tinubu Ya Tura Wa Jihar Ogun Buhunan Shinkafa 3,000 A Matsayin...

Shugaba Tinubu Ya Tura Wa Jihar Ogun Buhunan Shinkafa 3,000 A Matsayin Tallafi

32
0

Gwamnatin jihar Ogun, ta karbi buhunnan shinkafa dubu 3 na farko daga gwamnatin tarayya, domin cika alkawarin shirin ta na raba abinci ga ‘yan Nijeriya don rage tasirin cire tallafin man fetur.

Sakataren gwamnatin jihar Ogun Olatokunbo Talabi ya tabbatar da haka yayin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai, inda ya ce za a fara rabon shinkafar ne bayan an kammala shirin rabon.

Talabi ya kuma tabbatar da cewa, gwamnatin jihar ta karbo kudi daga gwamnatin tarayya domin sayen hatsi a wani bangare na kudin da aka tsara na sayen kayayyakin abinci da kowace jiha za ta raba wa mutanen ta.

Sakataren ya yi nuni da cewa, gwamnatin jihar ta na kara sayo hatsi domin karawa a kan wanda gwamnatin tarayya ta bada domin ya ishi mazauna jihar.

Ya ce tuni gwamnatin jihar ta kafa kwamitin mutane masu kishi da za su yi ruwa su yi tsaki wajen tabbatar da rabon kayan tallafin.