Home Labarai Shugaba Tinubu Ya Bada Umurnin Amfani Da Motoci Masu Iskar Gas

Shugaba Tinubu Ya Bada Umurnin Amfani Da Motoci Masu Iskar Gas

79
0
images (50)
images (50)

A wani mataki na cimma azamar sa na tsaron makamashi, da tsaftar muhalli da rage kashe kudaden sayen man fetur,

shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya umurci dukkanin ma’aikatu, da sashi-sashi da rassan gwamnati su sayi motoci masu amfani da Makamashin iskar Gas.

A cewar mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale,


umurnin na shugaban na cikin matakin tabbatar da tsaftar muhalli da karfafa amfani Motoci Masu amfani da Makamashin iskar Gas.

Iskar gas yana rage yawan kashe kudaden sayan man fetur.

shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya tabbatar da cewa babu komawa baya a shirin sa na rungumar Makamashin.

Shugaban kan sa ya kuma ba da umarnin kin amincewa da duk wasu takardu da ‘yan majalisar zartarwar suka gabatar,

Takardun suna neman sayan motocin gargajiya da suka dogara da man fetur,

inda ya umurci ’yan majalisar da abin ya shafa su koma su nemi hanyoyin sayan motocin da suka dace da CNG.

Sanarwar ta kara da cewa, shugaban kasa ya jajirce wajen amfani da karfin iskar gas ta kasa yadda ya kamata.

Tare da rage radadin tsadar sufuri a kan talakawa tare da inganta rayuwar dukkan ‘yan Najeriya.

Leave a Reply