Home Labaru Shugaba Buhari Ya Gana Da Shugabannin Tsaro

Shugaba Buhari Ya Gana Da Shugabannin Tsaro

111
0

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya gana da shugabannin fannin tsaro a fadarsa da ke nan Abuja.

Rahotanni sunce taron wata dama ce da za ta bashi damar tattara bayanai akan yadda harkokin tsaron ƙasar nan  ke gudana daga bakin jagororin.

Daga cikin wadanda suka Mahalarci taron sun haɗa da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Farfesa Ibrahim Gambari; Mai Bai wa Buhari Shawara Kan Sha’anin Tsaro, Major General Babagana Monguno (rtd), Shugaban rundunonin Tsaro, General Leo Irabor.

Saurana sun hada da shugaban sojojin ƙasa da na ruwa da na sama da kuma Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Usman Alkali Baba.

Leave a Reply