Home Labarai Shugaba Buhari Ya Gabatar Da Kudirin Dokar Kare Bayyanai a Majalisa

Shugaba Buhari Ya Gabatar Da Kudirin Dokar Kare Bayyanai a Majalisa

68
0
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya ba al’ummar Jihar Katsina haƙuri dangane da mawuyacin halin da ‘yan jihar da ma ƙasa baki ɗaya su ka shiga sakamakon canjin kuɗi da Babban Bankin Nijeriya ya yi.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci Majalisar
Dattawa ta amince da wani kudurin dokar kare bayyanai,
wanda sashen zartarwa na gwamnatin tarayya ya gabatar a
Majalisar.

Buhari ya bayyana bukatar ne a cikin wata wasika da ya aike wa Majalisar, wadda aka karanta a zaman da Majalisar ta yi a ranar Talatar da ta gabata.

A cikin wasikar, shugaba Buhari ya ce ya gabatar da kudirin dokar kare mahimman bayyanai ta Nijeriya a gaban Majalisar, domin ta yi nazari a kai sannan ta tabbatar da shi a matsayin doka.

Makasudin samar da wannan dokar dai shi ne, domin kare hakkin ‘yancin ‘yan kasa ta yadda ya shafi bayanan su kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanada.

Daga cikin wasu mahimman abubuwan da dokar ta kunsa, akwai batun tsarin yadda za a rika sarrafa bayyanan mutane, da inganta tsarin yadda za a gudanar da bayanan mutane ta hanyar da za ta kare tsaron bayanan su, da kuma samar da tsarin sirranta masu bayanan da kuma tabbatar da an mu’amalanci mahimman bayyanan da adalci ta hanyar shari’a.

Leave a Reply