Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kwatanta mutuwar Archbishop Desmond Tutu na Kasar Afirka ta Kudu a matsayin wani lamari da ya bar babban gibi a duniya.
Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya fitar, shugaba Buhari ya ce babban limamin cocin wanda ya yi fice a fannin kare hakkin bil adama ya rasu a daidai lokacin da duniya ke matukar bukatar hikimar sa, da jajircewar sa.
Shugaba Buhari, ya yi amannar cewa, mutuwar Archbishop Tutu, wanda ya har ila yau yi fice a fannin ilimantarwa, kwato hakkin bil adama, taimakawa mutane ta bude wani babban gibi ne a duniya.” Sanarwar fadar shugaban kasra ta ce.
Ya ce a madadin gwamnati da al’umar Najeriya, shugaba Muhammadu Buhari na mika sakon ta’aziyyar sa ga shugaba Cyril Ramaphosa, da al’umar Afirka ta Kudu da babbar kungiyar Kiristoci musamman ta Anglican bisa rasuwar Archbishop Emeritus Desmond Tutu.
Shugaba Buhari ya kuma jaddada irin rawar da marigayin ya taka wajen yaki da matsalar wariyar launin fata, da muzgunawa da ya fuskanta da ta hada da rufe shi da aka yi a gidan yari da kuma kaura da ya yi ta wani tsawon lokaci.
A ranar Lahadi 26 ga watan Disambar 2021, Archbishop Tutu ya rasu yana da shekara 90 a duniya.