Kungiyar kare hakkin Musulunci a Nijeriya MURIC, ta ce gwamnatin shugaba Buhari ba ta taba tauye ‘yancin addinai a Nijeriya ba.
Shugaban kungiyar Farfesa Ishaq Akintola, ya ce Amurka ta sa Nijeriya cikin jerin masu keta addini a shekara ta 2020 sakamakon bayanan karya da ta samu daga wasu ‘yan Nijeriya.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken dai ya sa Rasha da China da wasu kasashe takwas a cikin jerin masu keta ‘yancin addini, sannan ya cire Nijeriya da ke cikin jerin a shekara ta 2020.
Tuni dai ‘yan Nijeriya da kungiyoyi da dama da su ka hada da kungiyar kiristoci ta Nijeriya su ka nuna rashin amincewar su da hakan, inda su ka dage cewa har yanzu ana ci-gaba da tauye wa Kiristoci ‘yancin addini a Nijeriya.