Home Labaru Shugaba Buhari Ba Zai Sauya Tsarin Mulki Don Neman Tazarce Ba –...

Shugaba Buhari Ba Zai Sauya Tsarin Mulki Don Neman Tazarce Ba – Garba Shehu

451
0
Garba Shehu, Mai Ba Wa Shugaban Kasa Muhammdu Buhari Shawara Na Musamman Kan Harkokin Yada Labarai
Garba Shehu, Mai Ba Wa Shugaban Kasa Muhammdu Buhari Shawara Na Musamman Kan Harkokin Yada Labarai

Fadar shugaban kasa ta musanta rahotannin da ke cewa ana bukatar Shugaba Muhammadu Buhari ya yi tazarce a karo na uku.

Bayanin hakan, ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin shugaban kasa Garba Shehu ya wallafa a shafin sa na Twitter, inda ya ce shugaba Buhari mai kaunar mulkin demokradiyya ne, don haka ba zai taba yunkurin tsawaita wa’adin mulkin sa ba.

Ya ce shugaba Buhari zai sauka daga mukamin sa bayan kammala wa’adin sa na biyu a shekara ta 2023, kuma za a yi sabon zabe ba tare da ya sake tsayawa takara ba.

Garba Shehu ya cigaba da cewa, abu ne mai muhimmanci a gane cewa, a baya an yi yunkurin sauya kundin tsarin mulki, domin shugaban wancan lokaci ya yi wa’adi na uku, lamarin da ya ce ba daidai ba ne, kuma ya saba wa kundin tsarin mulki.

Ya ce babu wani yanayin da zai sa shugaba Buhari ya nemi gyara kundin tsarin mulki domin sauya wa’adin mulki na biyu  a matsayin shugaban kasa.