Home Labaru Shishshigi: An Kunyata Oshiomhole Saboda Saba Ka’ida Wajen Rantsar Da Buhari

Shishshigi: An Kunyata Oshiomhole Saboda Saba Ka’ida Wajen Rantsar Da Buhari

428
0

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomole ya kunyata, bayan ya tsaya tsakanin mukaddashin shugaban alkalan Nijeriya da shugabannin hukumomin tsaro a wajen bikin rantsar da shugaba Muhammadu Buhari da ya gudana a Abuja.

Oshiomole dai ya shiga sahun mataimakin shugaban kasa, da shugabannin majalisun tarayya da na hukumomin tsaro yayin jiran isowar shugaba Buhari a filin taro na Eagle Square da ke Abuja.

Hakan ya sa wani jami’in soji ya tunkari Oshiomhole, bayan takaitacciyar tattaunawa sai ya sauya wuri, yayin da babban hafsan hukumomin sojoji Abayomi Olonisakin ya maye gurbin da ya bari.

Duk da ya cigaba da tsayuwa a kan layin, Oshiomhole ya koma tsakanin shugaban rundunar ‘yan sanda Mohammed Adamu, da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha.

Leave a Reply