Home Labaru Ilimi Shirin Bayar Da Bashin Karatu Ga Ɗalibai Ba Mai Ɗorewa Ba Ne...

Shirin Bayar Da Bashin Karatu Ga Ɗalibai Ba Mai Ɗorewa Ba Ne – ASUU

135
0

Kungiyar malaman jami’o’i ta Nijeriya ASUU, ta buƙaci
Shugaba Bola Tinubu ya sauya dokar bada bashin karatu ga
dalibai da ya amince da ita, zuwa tallafin karatu domin a ba
ɗalibai masu ƙaramin ƙarfi damar samun ilmi mai zurfi.

A wata hira da gidan Talbijin na Channels, shugaban kungiyar ya ce bashin karatun ba abu ne mai yiwuwa ba, domin bada bashi don yin karatu ba zai dore ba.

Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce tunanin bada bashin karatu ga dalibai ya zo ne a shekara ta 1972, kuma ya na cikin harkokin bankuna da aka kafa, sannan mutanen da su ka karɓi bashin ba su taɓa biya ba.

Ya ce akwai dalibai sama da miliyan daya a jami’o’in gwamnatin tarayya, kuma rancen ba zai iya biyan kudin karatun su ba.

Leave a Reply