Home Labarai Shirin 2023: Bayan Ganawa Da Gwamnoni Osinbajo Ya Gayyaci ‘Yan Majalisun APC

Shirin 2023: Bayan Ganawa Da Gwamnoni Osinbajo Ya Gayyaci ‘Yan Majalisun APC

161
0

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, zai gana da
‘yan majalisar wakilai na jam’iyyar APC.

Osinbajo dai ya gayyaci ‘yan majalisun ne zuwa babban dakin
taro na fadar shugaban kasa domin buda bakin azumin watan
Ramadan a ranar Larabar nan.

Mataimakin kakakin majalisar wakilai Ahmed Wase ya karanta
wasikar da Osinbajo ya aike wa ‘yan majalisar.

Gayyatar dai ta zo ne, kasa da sa’o’i 48 bayan Osinbajo ya karbi
bakuncin gwamnonin jam’iyyar APC zuwa buda baki a daren
Lahadin da ta gabata, domin neman goyon bayan su a kan aniyar
sa ta takarar kujerar shugaban kasa.

Leave a Reply