Home Labaru Shigo Da Manja: Buhari Ya Umurci Gamnar CBN Ya Dau Mataki Akan...

Shigo Da Manja: Buhari Ya Umurci Gamnar CBN Ya Dau Mataki Akan Kamfanoni

451
0
Godwin Emefiele, Gwamnan Babban Bankin Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya umurci babban bankin Najeriya ya dau mataki akan kamfanonin dake shigo da manja da suke amfani dashi daga kasashen ketare.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele, ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da kungiyar masu samar da manja a Abuja.

Emefiele ya ce daga yanzu za a dauki kwararan matakai akan duk wadanda aka samu suna shigo da manja daga kasashen ketare, ta hanyar cire su daga duk wasu tsari na hada-hadar kudade da bankuna a ciki da wajen Najeriya. 

Ya ce wannan ya kunshi wadanda suka yi yunkurin shigo da manjan da wasu kayayyaki makamantan su ta kan iyakokin kasa.

Emefiele, ya kara da cewa a halin da ake ciki yanzu a fitar da naira billiyan 30 ga wadanda suka dukkufa wajen noman kwakwar manja domin inganta bangaren. Ya ce sabbin wadanda suka shigo harkar hada-hadar kasuwancin manja za su amfana da sabon tsarin da aka fito dashi domin kara musu kwarin gwiwar gudanar da ayyukansu.

Leave a Reply