Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Shigar Korona Fadar Shugaban Kasa: Adesina Ya Ce Shugaba Buhari Bai Kamu Ba

Fadar Shugaban kasa ta ce shugaba Muhammadu Buhari na nan lafiya lau bai kamu da kowace irin cuta ba.

Mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ne ya bayyana haka a lokacin da ya bayyana a shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Channelsa  ranar Lahadi.

Adesina ya ce shugaban ƙasa lafiyar sa ƙalau, kuma yana ci gaba da ayyukan sa kamar yadda ya saba.

Femi Adesina ya ce kamar yadda Garba Shehu ya tabbatar cewa shi ya kamu amma ya ce ba ta yi tsanani ba, dan haka ya yi imanin cewa zuwa yanzun ya kamata Garba Shehun ya warke tun da abin ya faru ne tun Laraba, Saboda haka babu wani abin tashin hankali.

Ya ce kamuwar wasu daga cikin ‘yan fadar shugaban kasan ba zai sa shugaban kasa ya kamu ba.

Exit mobile version