Shugaban Hukumar Kula da Ingancin abinci da Magunguna ta Kasa Moji Adeyeye, ta ce gwamnatin tarayya za ta biya diyyar sama da naira biliyan daya ga kamfanonin da aka kwace wa maganin ‘Codeine’ sama da shekara daya da ta gabata.
Moji ta bayyana haka ne a Lagos, yayin da ta ke karyata labarin da wata kafar yada labarai ta buga cewa hukumar NAFDAC ta ce kashi 70 cikin 100 na magungunan da su ka karade Nijeriya duk jabu ne.
Adeyeye, ta ce an kwace akalla kwalaben ‘Kodin’ miliyan biyu da rabi a fadin Nijeriya, amma ta ce gwamnati na aikin tantance kamfanonin tare da kokarin biyan su diyya.
Ta ce shekara daya kenan tun bayan wani bidiyo da aka yi a kan binciken yadda ake shan ‘Kodin’ a matsayin kwayar da ke bugarwa, lamarin da ya sa gwamnatin tarayya ta haramta maganin gaba daya.
Moji Adeyeye, ta ce tun daga lokacin jami’an gwamnati da ke da ruwa da tsaki a fannin da kamfanonin ke gudanar da tarurruka domin lalubo yadda za a samu mafitar biyan kamfanonin diyya.