Kungiyar masana kimiyyar hada magunguna na Nijeriya PCN, ta koka da yadda mutane musamman matasa ke hadiyar kwayoyi babu gaira babu dalili.
Rajistaran kungiyar Elisha Mohammed ya bayyana haka, a wajen taron tattauna hanyoyin da za a iya bi wajen kawar da wannan matsala a Nijeriya da ya gudana a Kaduna.
Mohammed, ya ce sakamakon wani kwakkwaran bincike da aka gudanar, ya nuna cewa akalla mutane miliyan 14 da dubu 400 ne ke tu’ammali da miyagun kwayoyi a Nijeriya.
Binciken, wanda aka gudanar a shekara ta 2019 ya kara nuna cewa, ‘yan shekaru 15 zuwa 64 ne su ka fi tu’ammali da miyagun kwayoyi a Nijeriya.
Ya ce lokaci ya yi da Nijeriya za ta maida hankali wajen kawar da wannan matsala, ganin cewa mafi yawan mutanen da ke tu’ammali da kwaya mutane ne da idan su ka gyaru za a samu ci-gaba a kasa.