Home Labaru Kiwon Lafiya Shaye-Shaye: Hukumar NDLEA Ta Kama Dillalin Miyagun Kwayoyi A Abuja

Shaye-Shaye: Hukumar NDLEA Ta Kama Dillalin Miyagun Kwayoyi A Abuja

114
0

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA, ta kama wani mutum da ake zargin kasurgumin dillalin miyagun kwayoyi ne mai suna Okey Eze, a filin sauka da tashin jirage na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

An dai kama Eze ne dauke da kunshi 350 na hodar Iblis, wanda
kudin su ya kai Naira biliyan biyu da miliyan 300.

Okey Eze, wanda dan asalin karamar hukumar Oji-River ne a
jihar Enugu, ya shiga hannun jami’an hukumar ne yayin da ake
tantance fasinjoji kafin shiga jirgin saman Ethiopian zuwa birnin
Addis Ababa.

Yayin da ya ke bayani, Okey Eze wanda mazaunin garin
Bamako ne na kasar Mali, ya ce ya zo Nijeriya da kwayoyin ne
don ya samu kudaden da zai kula da yaran dan’uwan sa da ya
mutu.

Shugaban hukumar NDLEA Burgediya Janar Buba Marwa mai
ritaya, ya ce hukumar za ta cigaba da yaki da masu yunkurin
maida Nijeriya matattarar ajiye miyagun kwayoyi.