Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Shaye-Shaye: Dillalan Kwaya Sun Kone Motar Jami’an Ndlea A Jihar Jigawa

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Jigawa, ta tabbatar da mutuwar wani matashi mai shekaru 25 Abubakar Lawan, bayan ya fada cikin wani Dam a kokarin guje wa jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a kauyen Sha-iskawa da ke karamar hukumar Kazaure.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Jigawa SP Abdu Jinjiri ya bayyana wa manema labarai haka a garin Dutse, inda ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 6 na ranar Larabar da ta gabata.

Jinjiri ya ce, marigayin ya fada cikin ruwan ne a kokarin sa na guje wa jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, yayin da su ka kai wani samame a wata mafakar masu dillancin miyagun kwayoyi.

Ya ce sakamakon mutuwar matashin, wasu fusatattun matasa sun afka wa jami’an hukumar tare da kone ofishin su.

Jinjiri ya cigaba da cewa, rundunar ‘yan sanda ta na gudanar da bincike domin ganin an kama masu hannu a cikin lamarin.

Exit mobile version