Home Labaru Shari’ar Zabe: Buba Galadima Ya Zama Shaidar Atiku Na Farko A Kotu

Shari’ar Zabe: Buba Galadima Ya Zama Shaidar Atiku Na Farko A Kotu

283
0

Injiniya Buba Galadima, ya zama mutum na farko da ya gabatar da shaida a gaban kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa a shari’ar da Atiku Abubakar ke kalubalantar nasarar shugaba Muhammadu Buhari.

Bayan jaddada matsayin shi na shugaban sabuwar jam’iyyar APC, Buba Galadima ya ce tun lokacin da su ka balle su ka kulla yarjejeniya da jam’iyyar PDP domin samar da kyakkyawan shugabanci.

Yayin da lauya mai kare shugaban kasa Wole Olanipekun ya tambaye shi game da matsayin ‘yar sa a gwamnatin shugaba Buhari, Buba Galadima ya ce ‘yar tasa tafi kowa ilimi a gwamnatin shugaba Buhari, kuma ta taka rawa wajen sake samun nasara a zaben da ya gabata.

lauya mai kare shugaban kasa Wole Olanipekun

A matsayin sa na shaidar farko da Jam’iyyar PDP ta gabatar, Buba Galadima ya nanata cewa har yanzu shi dan jam’iyyar APC ne, domin har yanzu babu wanda ya kore shi daga cikin ta.

Idan dai za a iya tunawa, a makon da ya gabata, Atiku Abubakar ya gabatar da shaidu dubu 26 da 175 na takardun kuri’un da aka jefa a wasu sassan jihohi 8 da su ka hada da Jigawa da Borno da  Gombe da Bauchi da Katsina da Kebbi da Kaduna da Kano.