Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kano Rabi’u Suleiman Bichi, ya gurfana a gaban kotun sauraren karar zaben gwamnan jihar domin bada shaida a kan kallubalantar nasarar Ganduje na jam’iyyar APC.
Sai dai Suleiman Bichi bai samu ikon bada shaidar a gaban kotun ba, saboda korafin da lauyan da ke wakiltar Ganduje da jam’ iyyar APC Aliyu Umar ya yi.

Barista Aliyu Umar ya shaida wa kotun cewa, kafin ranar Alhamis da ta gabata, bangarorin biyu sun cimma yarjejeniyar cewa ba za su gabatar da shaidu ba har sai an gyara wasu kura-kuren rubutu da kotun daukaka kara ta Kaduna ta yi magana a kai.
Ya ce bangarorin biyu sun amince da cewa, shugaban na PDP da wasu mutane bakwai za su bada shaida ne a ranar 5 ga watan Augusta, amma ya yi mamakin ganin sun gabatar da Sulaiman Bichi kotu a ranar 1 ga watan Augusta domin bada shaida.
Jagoran lauyoyin jam’iyyar PDP Awomolo ya shaida wa kotun cewa, a iya sanin sa, babu wata dokar kotu da ta haramta wa shugaban na PDP bada shaida, kuma ya roki kotu ta yi watsi da bukatar wadanda ake yi kara.
You must log in to post a comment.