Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin zaben Shugaban kasa, ta ce nan
gaba za ta bayyana ranar da za ta yanke hukunci a kan ƙarar
da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ya
shigar a kan Shugaba Tinubu.
Shugaban Kotun Haruna Tsammani ya bayyana haka, inda ya ce za a sanar wa ɓangarorin biyu ranar da za a yanke hukuncin.
AtikuAbubakar dai ya maka shugaba Tinubu da jam;iyyar APC da hukumar zabe kotu, inda ya ƙalubalaci nasarar Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa.
A zaman kotun, lauyan hukumar Abubakar Mahmoud, ya roƙi kotu ta yi watsi da ƙarar da Atiku ya shigar, domin a cewar sa, babu wasu hujjojin da Atiku ya badar, yayin da lauyan hukumar zabe ya ce an samu nasara wajen amfani da na’urorin BVAS da IReV a zaɓen shugaban ƙasa.
A nata bangaren, jam’iyyar APC ta roƙi kotu ta yi fatali da roƙon da Atiku ya yi, domin ya kasa gabatar da hujjojin da za su tabbatar shi ne ya yi nasara, da kuma maguɗin da ya ke cewa an yi masa.