Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Shari’a: Akwai Yiwuwar Hukumar Shari’ A Ta Sabunta Wa’adin Tanko Mohammed

Majalisar koli ta harkokin shari’a ta Najeriya ta fara wani babban taro domin tattaunawa akan yadda za ta shawo kan wanda za a nada a matsayin Alkalin Alkalan Najeriya.

Majalisar ta fara gudanar da taron ne a Abuja, manyan batutuwan da za ta dubu sun kunshi nadin Alkalin Alkalai na din-din-din.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa mai yiyuwa majalisar shari’ar ta sabunta wa’adin mai shari’a Tanko Muhammad a matsayin mukaddashin Alkalin Alkalai, zuwa lokacin da za ayi cikakken nadin kujerar.

Wa’adin Mohammed Tanko zai kare ne a ranar alhamis 25 ga Watan Afrilu, saboda dokar kasa ta ba  shi dama ne, ya yi rikon kwarya na watanni 3, inda wa’adinsa zai kare a makon gobe.

Kundin tsarin mulkin Najeriya, ya ce shugaban kasa bai da hurumin nada sabon Alkalin Alkalai ko kuma ya bada dama wanda ke kan matsayin rikon-kwarya ya ci gaba da rike kujerar ba tare da amincewar majalisar shari’a  ta kasa.

Alamu na nuna cewa mai yiyuwa majalisar shari’a ta Najeriya za ta yi na’am da cewa Muhammad zai ci gaba da rike wannan mukamin zuwa lokacin da za ayi nadin sabon Alkalin Alkalan.

Exit mobile version