Tun bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya sake zaben shi a matsayin gwamnan babban bankin Nijeriya, masu sharhi a kan tattalin arziki na ci-gaba da tsokaci a kan irin kalubalen da ke gaban Godwin Emefiele da kuma yadda zai yi ya shawo kan su.
Tuni dai majalisar dattawa ta tantance Emefiele, ta kuma amince ya sake komawa wa’adi na biyu, inda zai shafe tsawon shekaru biyar ya na jan ragamar bankin kamar yadda ya faro a shekara ta 2014.
Wani mai sharhi a kan tattalin arziki a Nijeriya Abubakar Aliyu, ya ce duk da cewa kwanakin baya hukumar kididdiga ta kasa ta ce Nijeriya ta fita daga matsin tattalin arziki, har yanzu akwai sauran rina a kaba game da batun hauhauwar farashi musamman na kayayyakin masarufi.
Ya ce dole ne babban bankin Nijeriya ya tabbatar bankuna sun bada bashi, musamman ga kamfanonin da ke sarrafa kayayyaki a farashi mai rahusa domin samar da kayayyaki, kuma dole a tabbatar an rage ba gwamnati bashi.