Home Labarai Sauyin Kudi: Sarkin Musulmi Ya Bukaci Shugaba Buhari Ya Dau Mataki

Sauyin Kudi: Sarkin Musulmi Ya Bukaci Shugaba Buhari Ya Dau Mataki

73
0

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauki matakan gaggawa na shawo kan wahalar da jama’a ke ciki a sanadiyyar sauyin kudi domin kauce wa bore.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Mai martaban ya nuna takaicin sa ne a jiya Litinin, inda ya nuna damuwa kan yadda jama’a suka fada cikin yanayi na yunwa da bacin rai saboda canjin kudin.

Ya ce matsalar sauyin kudin ta kara tsananta a tsakanin jama’a bayan da rahotanni suka nuna cewa bakuna sun daina amsar tsoffin takardun kudin na naira 200 da 500 da kuma 1,000.

A ranar Laraba da ta gabata ne Kotun Koli ta hana Babban bankin CBN aiwatar da tsarin sa na hana amfani da tsofaffin kudin a ranar 10 ga watan nan na Fabarairu, har sai ta yanke hukunci kan karar da gwamnonin Kaduna da Kogi da Zamfara  da Kano da Naija da Ekiti da kuma Ondo suka shigar a kan lamarin.

A gobe Laraba ne Kotun Kolin ta ce za ta yanke hukunci a kan karar wadda gwamnonin jihohin uku suka shigar.

Leave a Reply